An kara jami'an tsaro a Pilato

An kara tsaurara matakan tsaro a jihar Pilato mai fama da rikici, inda aka kara tura dakarun tsaro tare da nada sabon kwamanda manjo janar Oluwashewun Olayinka Oshinowo da zai jagoranci sha'anin tsaro a jihar.

Kwamitin hada - ka na jami'an dake magana da yawun hukumomin tsaro a Najeriya ya bayyana wa manema labarai haka a Abuja.

Haka kuma kwamitin ya ce an kori daya daga cikin jami'an sojin da ake zargi da sace mahaifin Michael Obi dan wasan kwallon Najeriya da kuma kungiyar kwallon kafa ta Chelsea daga aikin soji.

An dai kafa kwamitin ne domin rundunoni da hukumonin tsaro su yi magana da yawu daya kan sha'anin tsaro a kasar.