Kungiyar kwadago a Najeriya ta yi zanga zanga

Babbar Kungiyar Kwadago a Najeriya ta gudanar da wata zanga-zangar lumana don nuna goyon baya ga majalisar dattawan kasar dangane da wani bincike da ta fara a kan yadda aka sayar da wasu kamfanoni da kadarorin gwamnati.

Kungiyar ta ce, ta je harabar majalisar ne domin ta jaddada amincewarta da yadda kwamitin majalisar ke bankado wasu abubuwan da ta bayyana da badakala a harkar sayar da kamfanonin.

Haka kuma kungiyar tayi fatan za a hukunta dukkan wadanda aka samu da laifi.

Tun da farko dai an gargadi kungiyar da kada ta gudanar da zanga-zangar saboda halin tsaron da kasar ke ciki, amma ta ce sai ta yi.