Hannayen jari sun tuntsura -- bankin duniya kuma ya hango hadari

Kasuwannin hannun jari a duniya sun girgiza, suka yi kara warwas, bayan gargadin da aka samu daga Babban Bankin Amurka game da tattalin arzikin kasar.

Zuwa tsakiyar rana a yau, hannun jari a London da Paris ya yi kasa da kashi biyar cikin dari.

Su ma kasuwannin hannun jarin Asia sun kasan da bai kai yawan hakan ba.

Shugaban Bankin Duniya, Robert Zoellick, ya ce tattalin arzikin duniya yana cikin hadari.

Ya ce, "Duniya ta shiga yanki mai hadari. A shekarar 2008 mutane da dama sun ce ba su hango karatowar matsala ba. To yanzu dai shugabanni ba za su iya fakewa da hakan ba."