Najeriya zata goyi bayan 'yancin kasar Palasdinu

Taswirar Najeriya
Image caption Najeriya ta sake jaddada matsayinta na goyan bayanta ga 'yancin kan kasar Palasdinu

Yayinda shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas ke shirin gabatar da bukatar amincewa da kafa kasar Palasdinu ga kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya a yau, Najeriya ta sake jaddada matsayinta game da wannan batu

Minista a ma'aikatar harkokokin wajen Najeriya Dr. Nurudden Mohammad ya shaidawa BBC cewar matsayin Najeriya guda daya ne. Shine kuma palasdinawa na da 'yanci, kuma suna bukatar kasa ta kansu wacce zasu zauna a ciki babu mamaya

Ministan ya kuma yi watsi da rahotannin dake fitowa daga wasu kafafen yada labaru ba dake cewa Najeriya zata kasance 'yar baruwanmu, inda yace zance ne kawai na kangen kurege wanda kuma ba shi da wani tushe

Dr. Nurudden ya kara da cewar ra'ayin kasar Amurka daban, ta Najeriya daban game da wannan batu

Najeriya dai na daga cikin kasashen da aka zura ido domin ganin matsayin da zasu dauka dangane da wannan batu. Kuma a 'yan kwanakin nan wasu kafofin yada labaru na kawo bayanai masu karo da juna dangane da matsayin Najeriyar kan wannan batu.