Amurka ta zafafa suka a kan Pakistan

Jay Carney, kakakin fadar White House Hakkin mallakar hoto White House
Image caption Jay Carney, kakakin fadar White House

Amurka ta zafafa sukar da take yi wa Pakistan, tana zargin ta da barin masu tada kayar baya su yi aiki daga cikin kasar.

Wani kakakin fadar White House, Jay Carney, ya ce lalle ne Pakistan ta katse alakar da ke tsakaninta da kungiyar masu fafitika ta Haqqani, kungiyar da Amurka ke zargi da kai hari kwanan nan a kan ofishin jakadancinta a birnin Kabul.

Tun farko dai, ministar harkokin wajen Pakistan, Hina Rabbani Khar, ta gargadi Amirka a kan cewa tana kusa da yin asarar Pakistan a matsayin kawa, idan har ta ci gaba da cewa Pakistan din na goyon bayan masu tada kayar baya.