Putin zai sake takarar shugabancin Rasha

Hakkin mallakar hoto AP

Shugaban Rasha, Dmitry Medvedev ya sanar cewa ya kamata Pira minista mai ci yanzu, Valadimir Putin ya tsaya takarar zaben shugaban kasa na badi.

Mr Putin, wanda ya yi wa'adi biyu na shugaban kasa, ya bada shawarar cewa ya kamata Mr Medvedev din ya zama Pira minista bayan zaben 'yan majalisa da zaa yi a cikin watan Disamba mai zuwa

An bada wadannan shawarwarin ne dai a wajen babban taron Congres na jam'iyyar United Rasha mai mulkin kasar, kuma ta zo ne bayan watanni na cece-kuce game da dan takarar da zai tsayawa jam'iyyar a zaben na badi.