An yi jana'izar tsohon shugaban Afghanistan

Jana'izar tsohon shugaban Afghanistan

Asalin hoton, BBC World Service

Bayanan hoto,

Ranar Talata ne aka kashe Rabbani a gadansa da ke Kabul

An yi jana'izar shugaban majalisar sasantawa ta Afghanistan, kuma tsohon shugaban kasar Burhanuddin Rabbani, wanda dan kunar bakin wake ya kashe a birnin kabul.

An tsaurara matakan tsaro a wajen jana'izar wacce aka gudanar a fadar shugaban kasa - inda kuma shugaba Karzai ya halarta.

Daga nan ne kuma aka bunne gawar Rabbani cikin wani yanayi na dimuwa da jimami.

Rabbani, wanda shi ne shugaban Majalisar koli ta sasantawa a kasar, an kashe shi ne ranar Talata bayan da wani dan kunar bakin wake dauke da bom a rawani ya shiga gidansa a matsayin wakilin Taliban.

Ci gaba ta tattaunawa

Shugaba Hamid Karzai ya gayawa mahalarta jana'izar cewa zai ci gaba da shirinsa na samar da zaman lafiya a kasar.

"Jinin da aka zubar na wadanda suka yi shahada na bukatar mu ci gaba da yunkurinmu har sai mun samar da zaman lafiya," a cewarsa.

"Hakkinmu ne mu tunkari wadanda suke adawa da zaman lafiya."

Mr Karzai ya zargi wadanda suka kashe Rabbani da "manakisa da kuma yaudara", tare da cin zarafin Afghanistan da kuma sabawa sharudan addinin Musulunci.

Dan mamacin Salahuddin, ya shaida wa mahalarta jana'izar cewa: "Yau rana ce da muke shaida daya daga cikin munanan abubuwan da suka faru a tarihin siyasar wannan zamani."

Jama'a sun dimauce lokacin da gawar Rabbani ta isa wurin da za a bunne shi.

An kuma ji karar harbin bindiga amma 'yan sanda sun ce sun yi harbi sama domin tarwatsa dandazon jama'ar da ke jefa duwatsu kan ayarin motocin jami'an gwamnati.

Wasu daga cikin mutanen sun yi ta yin kalaman batanci ga Amurka da Pakistan da kuma shugaba Karzai.