Michael Sata ya lashe zaben shugaban kasar Zambia

Michael Sata Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Michael Sata ya lashe zaben shugabancin kasar Zambia bayan ya doke Shugaba Rupiah Banda

Babban alkalin kasar Zambia Ernest Sakala ya bayyana Jagoran 'yan adawar kasar Zambia Michael Sata a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar Zambia da aka gudanar, bayan da jam'iyyarsa ta kada jam'iyyar data shafe shekaru 20 tana mulkar kasar ta Shugaba Rupiah Banda mai ci.

Kwanaki biyu dai aka shafe an kirga kuri'un da aka kada, abinda ya haddasa tashin hankali a kasar inda matasa suka rika kone motoci da kuma kasuwanni a garuruwan Ndola da Kitwe dake da nisan kilomita dari biyu da hamsin daga arewacin Lusaka.

Mr. Sata dai ya samu kuri'u milliyan daya da dubu dari da hamsin da arba'in da biyar akan abokin hamayyarsa Shugaba Banda, wanda ya samu kuri'u dubu dari tara da sittin da daya da dari bakwai da casa'in da shidda.

Sata dai ya samu kashi arba'in da uku cikin dari na gabakidayan kuri'un da aka kada

Ana tsammanin Rupiah Banda mai shekaru 74 a duniya, kuma jagoran jam'iyyar MMD zai yi wani jawabi a yau juma'a game da zaben