Za'a cigaba da zaman shari'a a kasar Masar

Mohammed Tantawi Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Shugaban rikon kwaryar kasar Masar Mohammed Tantawi na fuskantar matsin lamba

Idan an jima a yau ne ake sa ran, Shugaban rikon kwaryar kasar Masar mai ci, Field Marshall Mohammed Hussein Tantawi, zai bada shaida a shari'ar da ake wa tsohon mai gidansa Hosni Mubarak.

Tsohon shugaban kasar dai na fuskantar zargin bada umurnin hallaka masu zanga- zanga, a lokacin da aka yi juyin juya hali bana a kasar, kuma zai iya fuskantar hukuncin kisa, idan an same shi da laifi.

Manema labaru sun ce Field Marshall Tantawi na fuskantar matsin lamba a cikin kasar, inda yake kokarin biyan bukatun sauye -sauye, ga kuma matsin lamba daga ketare, sakamakon tabarbarewar dangantaka tsakanin Masar da Isra'ila, bayanda zanga zanga ta barke sakamakon hallaka wasu sojojin Misrar da Isra'ilan ta yi.