Turkiyya ta kama jirgin ruwan Syria dauke da makamai

Bashar Al Asad, shugaban kasar Syria
Image caption Dangantaka tsakanin gwamnatin kasar Syria da Turkiyya na kara sukurkucewa

Yayinda yake yiwa manema labaru jawabi, Fira Ministan kasar Turkiyyan Recep Tayyib yace jirgin ruwan na dauke ne da tutar kasar Syria makare da makamai.

Sai dai bai ce ga inda aka kama jirgin ba, da kuma yaushe ba, amma ya lashi takobin cewar Turkiyyan zata kwace duk wani jirgin ruwan da ta sake gani a cikin ruwanta, ko kuma wanda zai wuce ta sararin samaniyar kasar ta

Wannan ba shi bane karo na farko a wannan shekarar da kasar Turkiyyan ta dakatar da jirgin kasar Syria dauke da makamai

Labarin abinda ya faru na baya- bayanan ya sake nuna alamar wata kullalliyar dake tsakanin kasashen biyu wadanda a wani lokacin a can baya abokanan juna ne.

Turkiyyan dai ta fusata sosai game da yadda gwamnatin Syria take kakkabe masu zanga- zanga a kasar da kuma kin tattaunawar sauye sauyen siyasa

A wata ganawa da suka yi a majalisar dinkin duniya da Shugaba Obama, Mr. Erdogan yace dangantakar kasarsa da Syria ta kare, kuma a farkon watan da ake ciki ne dai kasar Turkiyyan ta karbi bakwancin wani taro na fitattun 'yan adawar kasar Syrian