An gano gawarwaki sama dubu a Libya

Majalisar wucin gadin 'yan tawayen kasar Libya, NTC, ta bada sanarwar cewa ta gaano wani makaken rami a Tripoli dauke da gawarwaki dubu daya da dari biyu da 70. An yi imanin cewa gawarwakin na wasu fursunoni ne da jami'an tsaro suka karkashe a shekara ta 1996 a gidan kurkukun Abu Salim dake birnin na Tripoli.

Sabbin hukumomin Libyar sun ce sun gano inda aka binne gawarwakin ne, bayan da suka yi ma wasu gandirebobi tambayoyi, wadanda suka yi aiki a gidan kurkukun, lokacin da aka kashe mutanen, sakamakon zanga zangar da suka yi ta neman a kyautata masu yanayin zamantakewa.