Dakarun Libya zasu kaddamar da hare-hare a birnin Sirte

Birnin Sirte Hakkin mallakar hoto none
Image caption Dakarun gwamnatin Libya na shirin kaddamar da sabbin hare hare a cikin Sirte

Dakarun gwamnatin kasar Libya dake kai hare hare a birnin Sirte, daya daga cikin sauran inda magoya bayan Kanar Gaddafi suka rage, sun sake haduwa a cikin dare, kuma sun ce suna shirin kai sabbin hare hare a birnin, bayan gagarumar nasarar da suka yi a jiya asabar.

Bayan kwanaki da aka shafe ana kiki -kaka, dakarun majalisar rikon kwaryar kasar Libyan sun kaddamar da hare- hare na ba zata daga kudanci da kuma gabashi, inda rahotanni ke nuna cewa suna fuskantar tirjiya daga dakarun Kanar Gaddafi.

Wani mazaunin birnin mai sun Muhammad ya bayyanawa BBC cewa halinda ake ciki a Sirte shine tuni wasu suka tsere, kuma yace ana ci gaba da dauki ba dadi a wasu yankuna, tsakanin dakarun 'yan tawaye da na Kanal Gaddafi.