'Yan Najeriya dake kasar Libya na bukatar su komo gida

Taswirar Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu daruruwan 'yan Najeriya da rikici ya rusta dasu a kasar Libya na cikin wani mawuyacin hali yanzu haka

Wasu daruruwan 'yan Najeriya dake zaune a kasar Libya sun yi kira ga gwamnatin kasar ta kwaso su zuwa gida, saboda a cewarsu, suna cikin mawuyacin hali yanzu haka.

Sai dai a baya gwamnatin Najeriyar tace ta aike da jirage domin kwaso 'yan Najeriyar da rikicin na Libya ya rutsa da su.

Amma Kuma rahotanni na cewa, wasu 'yan Najeriyar da suka tsira sun sake komawa kasar.

Bincike dai ya nuna cewa wasu masu goyan bayan 'yan tawayen Libyan na cin zarafin bakaken fata 'yan Afurka.

Alhaji Muhammadu Labaran Sokoto wanda yanzu haka yake zaune a birnin Tripoli ya shaidawa BBC cewar ana yi masu kwacen kudi kuma a wasu lokuta sai sunyi roko kafin su samu abincin da zasu ci.

Ya kara da cewar yanzu haka abinda suke bukata daga gwamnatin Najeriya shine ta taimaka ta tura masu da jiragen da zasu dauko su