Matan Saudiyya zasu yi kananan zabuka

Sarki Abdullah na Saudiyya Hakkin mallakar hoto ab
Image caption Sarki Abdullah na Saudiyya

Sarkin Saudiyya, Abdullah bin Abdul-Aziz, ya yi alkawarin cewa a karon farko za a ba matan kasar damar shiga zaben kananan hukumomi nan da shekaru hudu masu zuwa.

Yanzu haka dai mata a Saudiyya ba su da 'yancin yin wasu abubuwa, ciki har da tukin mota.

Sarki Abdullah bin Abdelaziz ya ce yanzu maatan za su samu damar kada kuri'a, da ma tsayawa takara a zabe, yana mai cewa an cimma wannan matsaya ce, bayan tattaunawar da gwamnati ta yi da manyan malaman kasar.

Hakazalika, Sarki Abdullah ya ce matan zasu samu 'yancin shiga majalisar Shura.

Majalisar dai tana bada shawararwari ne ga gwamnati, kuma Sarkin ne ke nada mambobinta.