Dakarun NTC a Libya na durfafar Sirte

Dakarun majalisar wucin gadin 'yan tawayen kasar Libya, NTC suna karfafa farmakin da suke kai wa birnin Sirte, mahaifar Kanar Gaddafi, kuma rahotanni sun ce sun kusa cimma tsakiyar birnin.

Wani wakilin BBC dake tare da dakarun 'yan tawayen, kilomita 30 daga Gabashin birnin, ya ce ya ga fararen hula da dama suna tserewa daga birnin, kuma suna cikin halin dimauta da matukar damuwa.

Wakilin namu ya ce fararen hular ba su san ko dakarun 'yan tawayen sun je birnin don su yanto su ko kuma su tursasa masu ne.

A halin da ake ciki kuma, wani kakakin majalisar NTC ya zargi magoya bayan Kanar Gaddafi da kai hari a kan garin Ghadames mai dadadden tarihi, inda suka kashe mayakan 'yan tawaye 5.