Ana gwabza fada a kudancin Somalia

An yi ta gwabza fada a Kudancin Somaliya inda jiragen yakin Amurka marasa matuka da sojojin gwamnatin Somaliyar suka kai farmaki a kan dakarun kungiyar masu fafutuka ta al Al Shabaab.

Wadanda suka shaida al'ammarin sun ce jiragen yakin na Amirka sun yi ruwan bam a kan kauyuka uku, kusa da tashar jiragen ruwan Kismayo.

Garin na Kismayo dai, wata muhimmiyar hanya ce da ake bi don ficewa da kayayaki zuwa yankunan da ke karkashin ikon masu fafitikar na al Shebaab.

Rahotanni sun ce daya daga cikin jiragen yakin na Amirka ya yi hatsari, kuma kungiyar al Shabaab ta ce yanzu haka tana rike da jirgin.

A halin da ake ciki kuma, an bada rahoton sojojin gwamnatin Somaliyar sun yi artabu da mayakan kungiyar ta al Sahabaab a yankin Gedo na Arewacin kasar.