Malaman jami'o'i na yajin aiki a Najeriya

A Najeriya, yau ne kungiyar malaman jami'o'in kasar ta ASUU, ta fara wani yajin aikin gargadi na mako guda da nufin matsawa gwamnati lamba ta biya masu wasu bukatu, kamar yadda suka yi 'yarjejeniya da gwamnatin a shekarar 2009.

Kungiyar ta ASUU ta yi zargin cewa gwamnati ta yi kememe ta ki cika kusa kashi tamanin dabiyar cikin dari na 'yarjejeniyar da bangarorin biyu suka kulla.

Sai dai a martanin da ta mayar, gwamnatin Najeriya ta yi alkawarin biya wa malaman jami`o`in bukatunsu nan da watanni biyu masu zuwa.

Ma`aikatar kwadagon kasar ta bayyana cewa an yi zama da `ya`yan kungiyar tun a makon jiya, kuma an kafa wani kwamiti na musamman da zai duba yiwuwar aiwatar da yarjejeniyar da kungiyar ta cimma da gwamnatin tarayya.

Sai dai kungiyar ta ASUU ta ce baa cimma wata matsaya a zaman na makon jiya ba, kuma hakan ya nuna cewa gwamnatin ba da gaske take ba.