Kwamiti kan Boko Haram ya gabatar da rahoto

Arch Namadi Sambo
Image caption Mataimakin Shugaban Nigeria

Kwamitin da shugaban Nigeria, Dr Goodluck Jonathan, ya kafa domin duba hanyoyin magance rikicin boko haram ya gabatar da sakamakon bincikensa.

Kwamitin dai ya bada shawarar cewa akwai bukatar gwamnatin tarayya ta tattauna da kungiyar jama`atu ahlissunna lidda'awati wal jihad don samun maslaha.

Shugaban Jonathan ya kafa kwamitin ne mai mutane bakwai a cikin watan Agusta domin duba hanyar da ya kamata a bi domin warware wannan rikici da ya ki ci ya ki cinyewa.

Shugaban Kwamitin, Alhaji Usman Galtimari, ya shaidawa mataimakin shugaban Nigeria, Arch. Namadi Sambo cewar wajibi ne gwamnatin tarayya ta yi nazari akan matakin tattaunawa da sasintawa da 'ya 'yan kungiyar sannan kuma a duba hanyar shigar da su cikin sauran al'umma.