Sabbin dabarun shawo kan matsalar Girka

Euro
Image caption Akwai shakku kan yi wuwar aiwatar da wannan sabon shiri

Rahotanni sun ce Asusun bada Lamuni na duniya, IMF na fitar da sabbin matakan shawo kan matsalar tattalin arzikin da kasashen da ke amfani da kudin Euro ke fama da shi. Ana saran dabarun za su kunshi rage darajar basukan da ake bin Girka da kashi 50 cikin dari, a cewar editan BBC na fannin kasuwanci Robert Peston.

Shirin ya kuma kunshi fadada kudaden tallafi na kasashen na Euro zuwa euro tiriliyan biyu.

Gwamnatocin kasashen Turai na fatan kammala wannan shiri nan da makwanni biyar zuwa shida.

Aiwatar da wannan tsari wani jan aiki ne ga kasashen, acewar editanmu na fannin kasuwanci.

Sai dai ya kara da cewa gaza yin hakan, zai haifar da mummunan koma-baya a kasuwannin kudade wacce za ta dakile ci gaban tattalin arziki ko ma fiye da haka.

Har yanzu dai masu zuba jari ba su gamsu da yadda shugabanni suke tunkarar matsalar bashin ta Turai ba.

'babu wata takamammiyar hanya'

Masu lura da al'amura sun ce aiki ake bukata ba surutu ba, domin farfado da kasuwannin kudin.

A karshen mako kungiyar kasashe mafiya karfin tattalin arziki ta G20, ta nanata burinta na ganin "an hada karfi-da-karfe domin shawo kan matsalar", amma masu sharhi na ganin hakan ba zai wadatar da masu zuba jari ba.

"Ganin cewa babu wata takamammiyar hanya da kasashen na G20 za su bi wajen shawo kan matsalar, kungiyar ba za ta yi wani abin azo a gani ba wajen shawo kan matsalar," a cewar Mitul Kotecha na Credit Agricole.

Kasuwannin hannayen jari a Turai sun fadi a farkon budewarsu a ranar Litinin. Amma daga bisani sun tashi da kusan kashi 2 cikin dari a Jamus da Faransa.

Tunda farko kasuwannin Asia sun fadi, inda Nikkei ta Japan ta fadi da kashi 2 da digo 2, sai Hong Kong Hang Seng da ta fadi da kashi 1 da rabi, yayin da Kospi ta Koriya ta Kudu ta fadi da kashi 2 da rabi.