Shell ya rufe wata rijiyar mai a Najeriya

Kamfanin mai na Shell Hakkin mallakar hoto pa
Image caption Kamfanin mai na Shell ya dade yana aikin hakar mai a Najeriya

Kamfanin mai na Shell a Najeriya ya ce ya rufe wani wuri da yake hakar mai a yankin Naija Delta sakamakon karuwar sace-sacen mai da kuma sarrafa man ta bayan fage da wasu keyi a yankin.

Kamfanin ya ce hakan na nufin ya datakar da hako kimanin gangar danyen mai dubu ashirin da biyar da yake hakowa a kowace rana a wani wurin hakar mai a tsakanin jihohin Abia da jihar Rivers.

A sanarwar da ya fitar, kamfanin ya ce ba zai koma aikin harkar danyen man ba har sai an daidaita al'ummura a yankin.

Wani rahoto na baya-baya da hukumar makamashi ta duniya ta fitar ya nuna cewa Najeriya ce kasar da ta fi kowacce kasa a nahiyar Afrika fitar da man fetur inda takan fitar da danyen mai ganga miliyan biyu da dubu dari uku a kowace rana.

Kamfanin na Shell ya ce tun kimanin shekaru 2 da suka gabata ne ya gano cewa wasu `bata gari na sace man a wurin da kamfanin ke harkar man.

Sai dai a 'yan watannin baya jami'an tsaro sun shawo kan lamarin bayan da suka abkawa masu sace man suka kuma lalata jiragen ruwa da sauran kayayyakin da suke amfani wajen yin wannan aika-aika.

Sai dai a cewar kamfanin duk da girke jami'an sojojin kasar a yankin Neja Deltan wadanda suka yi nasarar bankado wasu wuraren da ake sacewa tare da sarrafa danyen man ta bayen fage, a 'yan kwanakin nan an sake komawa gidan jiya inda ake sace man ba kakkautawa.

Kamfanin ya ce mutanen dake satar man na amfani ne da zarto mai kaifin gaske wajen fasa bututun man, inda suke makare kananan kwale-kwale da danyen man har kimanin dubu 40 da sukan sace.

A watan da ya gabata ne ma kamfanin na Shell ya rufe daya daga cikin tashohin da ya ke sarrafa iskar Gas dake Utorogu a yankin Neija Delta sakamakon yoyon da aka samu a daya daga cikin bututun mai na kamfanin.

Farfasa bututun mai a Najeriya matsala ce da ta zama tamkar ruwan dare a yankin Neja Delta mai arzikin man fetur, lamarin da yasa kamfanonin mai a yankin da suka hada da Shell dakatar da aikace-aikacensu a 'yan shekarun nan.