Takaddama tsakanin Brazil da FIFA

Hakkin mallakar hoto Reuters

Wata takaddama tsakanin hukumar wasan kwallon kafa ta duniya -FIFA, da kuma Brazil game da shirye shiryen gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a shekara ta dubu biyu da 14 ga alama ta tsananta.

Shugabar Brazil Dilma Roussef ta bukaci ganawa da shugaban hukumar kwallon kafar ta duniya, Sepp Blatter domin abinda ta kira tattaunawar gaskiya.

Hukumar ta FIFA wadda ke sa ran yin iko da baki dayan jerin wasannin cin kofin , an yi amannar ta na adawa da shirin Brazil na yin rangwame ga tikitin shiga kallon wasannin ga dalibai da kuma tsofaffi.

Wani batun kuma shi ne na aniyar Brazil na barin gidajen telbijin na kasar su nuna wasu wasanni.