Rikicin bashi: Girka na neman tallafin Jamus

Rikicin euro
Image caption Kasashen Jamus da Faransa ne kan gaba wajen ceto Girka

Fira ministan, Girka George Papandreou, ya yi kira ga 'yan kasuwar Jamus da su taimaka wa kasarsa ta fita daga cikin matsalar bashin da ta ke fama da ita.

Mr Papandreou ya ce kudaden Jamus ba za su kasance asara ba, sai dai wani jari da za a ci ribarsa nan gaba.

Ya yabawa kasar dangane da yadda ta ke kokarin shawo kan matsalar bashin da ke kan ta.

Fira ministan yana magana ne a Jamus bayan tattaunawar da ya yi da shugabar gwamnatin kasar, Angela Merkel, domin tattauna ci gaban da aka samu a matsalar bashin kasar.

Sai dai a nata bangaren, shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel, ta ce matsalar da ake fama da ita ta bashi ce, ba takardar kudin bai-daya ta euro ba.

Ta yi watsi da kalaman da ke cewa, akwai bukatar fadada kudaden tallafi domin kaucewa matsalar, tana mai cewa wannan ba zai yi wu ba.

'zai taimaka matuka'

Mr Papandreou ya ce: '' Wannan matsalar ta bayar da muhimmiyar dama da aiwatar da sauye-sauye masu mahimmanci da Girka ke matukar bukata. Taimakonku zai taimaka matuka".

"Taimakonku zai taimaka matuka", kamar yadda ya shaida wa taron 'yan kasuwar kasar ta Jamus.

Mr Papandreou ya ce a shekara ta 2010, Girka ta rage gibin kasafin kudinta da kashi biyar cikin dari.

Don haka, ya ce nan da shekara ta 2012, kasar za ta samu rara a kasafin kudinta.

Ziyarar Mr Papandreou na zuwa ne a daidai lokacin da shugabanni Hukumomin Kudi ke shirin yanke hukunci kan yiwuwar sakin kudaden tallafi na baya-bayan nan da aka yi wa Girka alkawari.

Hukumar Tarayyar Turai, da Babban Bankin Turai (ECB), da kuma Asusun bayar da Lamuni na Duniya (IMF) za su kai ziyara Girka a wannan makon, domin ganin irin ci gaban da kasar ta samu.

Karin bayani