An nemi da a sa ido akan manyan makamai a Libya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojojin Majalisar rikon kwarya na tunkarar Sirte

An yi kira ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya tsaurara matakai domin hana masu tsatsauran ra'ayi samu makamai daga Libya.

Shugaban hakar Siyasa a Majalisar, Lyne Pascoe ya ce, dolene a tsaurara tsaro ga wuraren da ke dauke da makaman kare dangi da kuma makami mai linzami da ake harbo jirgin sama da shi.

Mista Pascoe ya ce yana da mahimmaci sabuwar gwamnati rikon kwarya a Libya da kuma kawayen ta, su tabbatar da tsaro a wuraren da dakarun Kanal Ghaddafi su ka baro manyan makamai.

Jami'in ya ce kamata ya yi a kara maida hankali wuraren ajiyan makaman kare dangi.

Ya ce akwai damuwa matuka, idan 'yan ta'adda su ka samu irin wadannan makamai, musamman ma yadda ake cikin wani yanayi na rashin tabbas a kasar.

Akwai rahotannin dake nuni da cewa tuni dai aka fara siyarda wasu makaman da su ka fito daga Libya a wasu kasashe.

A yanzu haka dai, Sojojin Majalisar rikon kwarya ta Libya sun samu shiga cikin garin haihuwar Kanal Gaddafi wato Sirte daga gabashin garin, bayan kusan kwanaki uku ana gwabza fada da sojojin dake biyayya ga Kanal Gaddafi.

Sojojin Majalisar da masu biyayya da Kanal Gaddafi na ta harba rpkoki ne a tsakaninsu a gabashin bayan garin.

Wannan dai ya biyo janyewar da Sojojin Majalisar rikon kwaryar su kayi daga yammacin garin kwanaki biyu da su ka wuce bayan da su ka fuskancin turjiya daga Sojojin da ke biyayya ga Kanal Gaddafi.