Biritaniya tana tsaurara iznin zama kasar

Damian Green Hakkin mallakar hoto other
Image caption Yanzu karatu sai kana jin Ingilishi

Gwamnatin Biritaniya tana gabatar da sabbin dokoki domin maganin masu yin auren bogi don neman iznin zama kasar.

Haka kuma za a tsawon lokacin da mutum zai yi aiki a kasar kafin ya sami iznin zama.

Zuwa kara karatu kuma sai mai jin Ingilishi sosai.

Ministan harakokin shige da ficen Britaiyar, wato Mr Damian Green, shi ya fadi hakan a wata lacca da ya bayar a Jami'ar Legon da ke birnin Accra a yau a ci gaba da ziyarar wasu kasashen yammacin Afrika da yakeyi.

Haka kuma kasashen Ghana da Britaniya sun fara tattaunawa a kan yiyuwar dawowa da frusunonin Ghana da ke tsare a gidajen yarin Britaniyar zuwa gida don su ci gaba da zaman kaso a Ghanan har wa'adinsu ya cika.

A farkon wannan makon ne dai gwmnatin Britanian ta cimma yarjejeniya da Nigeria kan hakan dangane da fursunonin Nigerian dake can.