CAN 2013: Afrika ta Kudu ta maye gurbin Libya

Caf
Image caption Wannan gasa na da muhimmanci ga kasashen Afrika

Hukumar kula da kwallon kafa ta Afrika Caf ta amince da Afrika ta Kudu ta dauki bakuncin gasar cin kofin Afrika a shekara ta 2013 maimakon Libya.

Libya ta fasa shirya gasar ne saboda rikicin da ta ke fama da shi.

A lokacin da aka kulla yarjejeniyar Caf ta ce ba ruwanta saboda Najeriya da Aljeriya sun nuna sha'awarsu ta daukar bakuncin gasar.

A yanzu Libya ce za ta dauki bakuncin gasar a shekara ta 2017, wacce aka tsara yi a kasar Afrika ta Kudu.

Afrika ta Kudu za kuma ta maye gurbin Libya wajen shirya gasar cin kofin Afrika ta 'yan wasan da ke taka leda a cikin gida.

Hukumar dai a baya ta shirya kada kuri'ar zabar kasar da za ta dauki bakuncin gasar ne a ranar Laraba.

Amma sai kwamitin gudanarwar ta wanda ke taro a kasar Masar, ya amince da Afrika ta kudu a maimakon Najeriya, wadda itama ke takarar daukar nauyin bakuncin gasar.

Caf ta kuma bayyana cewa Namibia za ta karbi bakuncin gasar cin kofin Afrika ta mata, sannan kuma Nijar na 'yan kasa da shekaru 17 a shekara ta 2015.

Madagascar kuma za ta shirya gasar cin kofin kwallon kafa ta matasa 'yan shekara 17 a shekara ta 2017, sannan kuma na 'yan kasa da shekaru 20 a Senegal.