Yan adawa da gwamnati na takun saka a Gombe

Taswirar Najeriya
Bayanan hoto,

Taswirar Najeriya

'Yan adawa a jihar Gomben Nijeriya na barazanar kai gwamnatin jihar kotu saboda da gwamnnan jihar, Alhaji Hassan Ibrahim Dankwambo, bai nada kwamishinoni ba.

'Yan adawan, suna masu cewa yanzu ana gudanar da mulkin jihar ce tamkar mulkin kantoma.

To sai dai kuma gwamnan na jihar Gombe cewa yake yi 'yan adawar na gajen hakuri ne kuma babu wani lokaci da kundin tsarin mulki ya kayyade cewa lallai gwamna ya nada kwamishinoninsa.

Alhaji Audu Baba, shugaban jam'iyyar adawa ta CPC a jihar ya ce; " A gaskiya ba'a bi tsarin mulki ba, ana tafiyar da mulkin kantoma ne kawai a kasar.

"Ana bada kwangiloli kuma ana tafiyar da wasu ayyukan gwamnati ba tare da kwamishinoni ba, abun da kuma bai da ce ba."

Sai da kuma shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin a Jihar, Alhaji Ahmed Yayari, ya kare matakin gwamnati inda ya ce gwamnati na nazarin mutanen kwarai ne domin ta tantance su.