Girka ta yi sabuwar doka kan harajin gidaje

Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Fira Ministan Girka, George Panpandreou

Majalisar Dokokin kasar Girka ta amince da wata sabuwar doka a kan harajin gidaje, wadda ake ganin za ta taimaka wajen samarda kudaden da za su taimakawa kasar wajen sauke nauyin basusukan da ke kanta.

Dokar wadda ake takkadama a kan ta an awaitar da ita ce, wasu 'yan kwanaki, kafin ziyarar masu binciken kudi daga Tarrayar Turai da kuma Asusun bada lamuni na duniya, kasar.

Ziyarar masu binciken kudi daga Tarrayar Turai da kuma Asusun bada Lamuni na Duniya zawa Girka, zai ba su wata dama ce, da za su yi nazari game da shirye shirye tsuke bakin aljihu da kasar ta yi, saboda a san irin tallafin da za'a baiwa kasar.

Majalisun Dokoki a kasar Finland da kuma Jamus za su kada kuri'a cikin wasu 'yan kwanaki, kan irin karin talafi da kasashen za su iya badawa a gudunmuwar da Tarrayar Turai ke baiwa Girka.

Tun farko dai, kasuwannin hanayen jari na ci gaba da tashi, abun da kuma ke la'akarin da irin shirin da kasashen Tarrayar Turai ke yi domin ceto tattalin arzikin yankin.

A wani bangaren kuma Fira ministan, Girka George Papandreou, ya yi kira ga 'yan kasuwar Jamus da su taimaka wa kasarsa ta fita daga cikin matsalar bashin da ta ke fama da ita.

Mr Papandreou wanda ya yi kiran a wata ziyara da ya kai kasar Jamus ya ce kudaden Jamus ba za su kasance asara ba, sai dai wani jari da za a ci ribarsa nan gaba.