Amurka ta sa ma wasu kungiyoyi takunkumi

Hillary Clinton Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton

Jami'an gwamnatin Amurka sun bayyana sabon takunkumin a kan abin da suka kira kungiyoyin 'yan ta'adda masu hadarin gaske da ke kai hare-hare daga Afghanistan da Pakistan.

Takunkumin - a kan wasu mutane biyar - ya zo ne a lokacin da Amurka ke zargin Pakistan da goyon bayan kungiyar Haqqani, wadda ake zargi da kai hari a kan Amurka a yankin. Take kuma kira a kan Pakistan da ta dauki mataki a kan kungiyar.

Firaministan Pakistan dai, Yusuf Raza Gilani, ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa, dukkan wadannan kalamai da ke fitowa daga Amurka abin mamaki ne gare su.

Ya ce sun saba wa sadaukarwar da Pakistan tai ta yi a duk tsawon shekarun nan.