Jamus za ta kada kuri'a kan bada tallafi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kadin Euro na fuskantar koma baya

A yau Laraba ne, Majalisar Dokokin Jamus za ta kada kuri'a a kan ko za ta goyi bayan karfafa asusun ba da tallafi ga kasashen da ke amfani da kudin euro, a yunkuri na baya-bayan nan na magance matsalar karayar bashin da ta ddabi yankin.

Kudirin dai zai baiwa asusun ba da tallafin wanda aka fi sani da EFSF karin kudi da iko don tallafawa kasashen da bashi ya yiwa katutu irinsu Girka.

Ana dai sa ran wasu daga cikin wakilan jam'iyyun da ke cikin gwamnatin gamin gambiza ta Angela Merkel za su kada kuri'ar kin amincewa da kudirin.

Idan wakilai fiye da goma sha tara suka juya mata baya, to Angela Merkel za ta dogara ne a kan 'yan adawa don samun kuri'un da ta ke bukata.

Sai dai ko da yake za ta yi nasarar amincewa da kudirin, hakan zai jawo mata rauni a siyasance.

Nauyi

Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, William Hague, ya kwatanta kasashen Turai masu amfani da kudin euro da wani gini da ya kama wuta amma kuma ba shi da wata mafita.

A yayin da shugabannin kasar Turai ke kokarin shawon kan matsalar bashin da ta addabi wasu kasashe, Mista Hague ya zama wajibi Jamusawa su dauki nauyin kasashen da ke amfani da euro masu rauni irin Girka har karshen rayuwarsu.

Ana cikin haka ne kuma sai kamfanin akantoci na kasa-da-kasa, Ernst and Young ya fitar da wani hasashe mara dadin ji a kan tattalin arzikin kasashen da ke amfani da euro.

Wata jami'a a kamfanin, Marie Diron, ta ce lamarin ya tabarbare matuka:

"Tun bayan da muka wallafa rahoton mu na baya-bayan nan watanni uku da suka gabata abubuwa sun kara tabarbarewa sosai.

"Abin da muke gani yanzu shi ne rashin bunkasa da kuma yiwuwar koma bayan tatttalin arzikin wadannan kasashe badi."