An jefi jakadan Amurka a Syria ta tumatur

Robert Ford Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jami'an tsaro a kofar ofishin Hassan Abdul Azim

Magoyan bayan shugaban Syria sun jefi jakadan Amurka a Syria Robert Ford da tumatur da `kwai a lokacin da ya ke ganawa da jami'an 'yan adawa a birnin Damascus.

Gogaggen dan siyasa Hassan Abdul Azim ya ce akalla masu zanga-zanga 100 ne su ka yi kokarin kutsa kai ofishinsa a lokacin da Mr Ford ya isa wurin, sannan su ka yi garkuwa da su a ciki.

Jami'an Amurka sun ce "lamarin wani tashin hankali ne" kuma ya lalata motocin ofishin jakadancin, amma ba abinda ya samu Mr Ford.

Tunda farko dai Syria ta zargi Amurka da ingiza jama'a su yiwa sojojinta bore.

"Kalaman baya-bayan nan da Amurka ta fitar sun nuna a zahiri....Amurka na da hannu wajen ingiza masu dauke da makamai su kaiwa sojojinta hari," a cewar wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen Syria.

Ana ganin sanarwar na nuni ne da kalaman wani mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Mark Toner, wanda ya ce "ba abin mamaki ba ne idan 'yan adawar Syria su ka yi bore ga sojojin kasar".

Mr Ford ya fusanta Damascus a baya, musamman saboda ziyarar da ya kai birnin Hama tare da takwaransa na Faransa a watan Yuli.

Hakan ya sa magoya bayan shugaba Assad sun kaiwa ofisoshin jakadancin Faransa da na Amurkan hari.