An kame darururwan 'yan adawa a Guinea

Image caption Shugaban kasar, Guinea Alpha Conde

Jami'an tsaro a kasar Guinea sun kame daruruwan 'yan adawa a babban birnin kasar, Conakry.

A wata hira da ya yi da BBC, babban jagoran 'yan adawar kasar, Cellou Dalein Diallo, ya ce an tsare 'ya'yan jam'iyyarsa su fiye da dari biyar.

Mutane biyu ne dai suka rasa rayukansu a wata taho-mu-gama da aka yi tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanaga a farkon wannan makon.

Gwamnatin kasar ta Guinea ta yi kira ga 'yan adawar da su hau teburin shawarwari.

Mista Diallo, wanda ya sha kasa a zaben shugaban kasar da aka gudanar bara, ya yi korafi a kan zabukan majalisun dokokin da za a gudanar a watan Disamba.

Yana mai cewa zaben ba zai yi tasiri ba saboda tuni aka riga aka tafka magudi.