Interpol ta bada sammacin Sa'adi Gaddafi

Sa'adi Gaddafi Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Muammar Gaddafi

Hukumar 'yan sanda ta duniya, Interpol, ta fitar da sammacin kama Sa'adi Gaddafi, dan tsohon shugaban Libya, Kanar Mu'ammar Gaddafi.

Interpol tana zarginsa ne da aikata wasu laifuka a lokacin da yake jagorancin hukumar kwallon kafar kasar.

Interpol ta ce ta fitar da sanarwa - wadda ke daidai da ayyana cewa mutumin yana cikin wadanda aka fi nema a duniya ruwa a jallo.

Kuma sabuwar gwamnatin wucingadi ta Libya ce ta nemi a yi hakan.

Gwamnatin jumhuriyar Nijar dai ta tabbar cewa Sa'adi Gaddafi yana cikin Nijar din.

Tuni dama Hukumar Interpol ta fitar da irin wannan sanarwa a kan tsohon jagoran jami'an ayyukan sirri na Libyar, Abdullah Al Senussi.