An yi taron addu'o'in zaman lafiya a Najeriya

goodluck Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Ofishin Hukumar wayar da kan jama'a ta kasa a Najeriya wato NOA, ta shirya wani taron gangamin addu'a a baki dayan Jihohin kasar game da matsalar tsaro.

An dai shirya wannan gangami ne da taimakon shugabannin addininai na kasar, domin yin addu'a don shawo kan matsalar tsaro da ta yiwa kasar dabaibayi.

An kuma an umarci al'ummar Najeriya da su bar duk abinda suke yi da misalin karfe sha biyu na rana, domin yin tasu addu'a game da wannan matsala.