Sarki Abdullah ya soke hukunci bulala a kan wata mata

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An dai haramtawa mata tukin mota a kasar Saudiyya

Sarki Abdullah na kasar Saudi Arabia ya soke hukuncin bulala goma da aka yiwa matar nan da aka samu da keta dokar hana mata tuki a daular kasar.

Wani jami'in gwamnati ne ya tabbatar da soke hukuncin da Sarkin ya yi.

Masu fafutukar kare hakkin mata dai, sun ta kai komo a 'yan kwanakin da su ka wuce da nufi ganin a soke hukucin.

Gimbiya Amira al- Taweel matar Yarima Al-Waleed bin Talal a kasar ta Saudiyya ta nuna farin cikin ta a shafin ta na twitter game da soke hukuncin da sarkin ya yi.

Ta rubuta cewa ne a shafin ta, na yi amanar cewa mata da dama a Saudiyya su na cikin farin ciki, saboda soke hukuncin da aka yi, kamar yadda nima ke cikin farin ciki.

A ranar Talata da ta gabata ce aka samu, Shaima Jastaniah, da laifin tuki a birnin Jedda a watan Yulin da ya gabata.

Kungiyoyin mata da dama ne su ke shirya gangami domin adawa da dokar hana mata tuki a kasar ta Saudiyya.

Saudiyya ce kadai kawai kasa a duniya da ta haramtawa mata tukin mota.

Babu dai doka a rubuce da ta haramtawa mata yin tukin mota a kasar.

Ministan harkokin cikin gida ne ya bayyana dokar hana mata tuki, bayan da wasu mata su ka gudanar da zanga zanga a watan Nuwanban shekarar alif dari tara da casa'in su na tuka motoci a kasar.