Obama ya yi farin ciki da kisan Al-Awlaki

Anwar Al-Awlaki Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tuni shugaba Obama ya bada umarnin a kashe Al-Awlaki

Shugaba Obama na Amurka ya tabbatar cewa an kashe daya daga cikin 'yan kungiyar Alqa'ida da ya fi tasiri, Ba'amerike, Anwar Al-Aulaqi.

A Yemen ne aka kashe shi.

An ce Al-Awlaqi ya taka muhimmiyar rawa wajen shiryawa da ba da umurni kisan Amerikawa.

Shugaba Obama ya bayyana farin cikinsa da kisan Al Awlaqin.

Ya ce, "Mutuwar Al-awlaqi babban gaci ne aka kai a babban yakin da ake yi da Alqa'ida da kuma sauran kungiyoyi kawayenta.

Jiragen yakin Amurka da kuma jirage marassa matuka a Yemen sun kai wa jerin gwanon motocinsa hari.

Tun farko rahotanni sunce an kai farmakin ne a tsaunukan da ke da nisan kilomita 140 gabas da birnin Sanaa babban birnin kasar.

Hakan ya biyo bayan wani umurnin da Shugaba Obama ya sanya wa hannu a bara na nemowa da kuma kashe Awlaki, wanda dan kasar Amurka ne.

Ana zarginsa da laifuka da dama

Anwar Al Awlaki ya yi suna ne ta laccocinda ya ke yi da kuma ra'ayoyinsa da ake wallafawa ta shafukan internet, inda ya ke yin kira da akai hare-hare a kan wadanda ya kira maikya addinin musulunci.

An kuma san shi da kushe shugabanin kasahen Larabawa. A wata lacca da ya gabatar ya kakkausar suka a gare su:

"Wadannanan sarakunan da shugabannin kasashen Larabawa basu cancanci shugabancin ko wacce kasa ba. Kai ba su ma dace da kiwon garken awaki ba," a cewarsa.

Sanarwar kisan sa babu shakka wata babbar komabaya ce ga kungiyar Al-ka'ida tun bayan kisan Osama bin Laden a watan Mayu.

A bara ne Shugaban Amurka Barrack Obama ya bada wani umarni mai cike da kace-nace na hallaka Al-Awlaki duk inda aka ganshi.

Ana dorawa Al Awlaki lafin hare-haren da wasu suka kai a Amurka da Turai.

Ga misali ana ganin shi ne ya karfafawa wani sojan Amurka, Manjo Hassan Nidal gwiwa, har ya kashe wasu abokan aikinsa a Texas.

Hakazalika ana zargin sa da karfafawa wata 'yar Burtaniya Roshorana Chaoudry Gwiwa har ta dabawa dan majalisa Stven Timms wuka don ya goyi bayan harin da aka kaiwa Iraqi.

Al-awlaki yana da kwarjini. Ya kuma nak`anci Turancin Ingilishi don haka zai yi wuya ga Alqaeda ta maye gurbinsa.