Sojoji a Syria na taimakawa masu zanga zanga

Ana ci gaba da kabsawa tsakanin masu zanga-zangar kyamar gwamnatin Syria da kuma jami'an tsaron kasar a kewayen garin Rastan.

An samu karin zanga-zanga a duk fadin kasar a yau bayan sallar Jumma'a.

Masu fafitika sun ce an kashe mutane akalla goma sha biyar a garin na Rastan, a cikin kwanaki hudun da suka wuce.

Kafofin watsa labaran gwamnatin Syria sun ce an kashe sojoji bakwai.

Rahotanni daga Rastan din sun ce soji da dama da suka sauya sheka suna taimakawa jama'a wajen fafatawa da sojin gwamnatin.