Kungiyar Alk'a'ida ta yi babban rashi

Anwar Al-awlaki Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Anwar Al-awlaki

Jami'ai a Amurka da Yemen sun ce, daga cikin 'yan Alqa'ida da suka fi karfin fada a ji, an kashe haifaffen Amurkan nan, Anwar Al-aulaki.

Sun ce jiragen yakin Amurka ne suka kai hari da jirgi marar matuki a kan ayarin motocin da yake ciki a kasar Yemen.

Al-Aulaki ya dai yi suna ne daga laccoci ta bidiyo da intanet da yake yi, yana karfafa gwiwar a kai hari a kan kasashen Yamma.

Ya ce,Inda yake cewa yaki da shedan bai bukatar wata fatawa, bai bukatar shura, bai bukatar istikhara. Su rundunar Shedan ne. Yakar su shi ne abin yi a wannan lokaci.

Kisan nasa dai ya biyo bayan dokar da shugaba Obama ya sanya ma hannu bara, da ta nemi a nemo, tare da kashe Al-aulaqi, wanda dan Amurka ne.