NATO ta kama Kwamandan Kungiyar Haqqani

Dakarun kungiyar NATO a Afghanistan
Image caption Dakarun kungiyar NATO a Afghanistan

Rundunar sojojin kawance dake karkashin jagorancin kungiyar NATO a Afghanistan, ISAF ta ce ta cafke wani babban kwamanda na kungiyar Haqqani, wadda aka dorawa alhakin wasu jerin hare-hare a kasar.

Wakilin BBC ya ce kungiyar NATO ta ce Haji Mali Khan, yana dauke muggan makamai, amma bai nuna wata tirjiya ba a lokacin da dakarun NATO din suka je kama shi, tare da wasu masu fafutukar.

NATO ta ce, kamun Haji Mali Khan, wani babban cigaba ne a kokarin da take yi na kawar da kungiyar ta Haqqani, wadda, a kwana nan ta kai harin a kan Ofishin jakadancin Amirka dake birnin Kabul.

Kungiyar ta Haqqani, wani reshe ne na kungiyar Taliban, wadda ta musanta cewa an kama Mali Khan.