An kama mutane sama da 80 a Kamaru

Rundunar sojin Kamaru ta kama mutane fiye da tamanin a kudancin kasar.

Wani wakilin BBC ya ce fiye da rabin mutanen da aka tsare, 'ya'yan wata kungiya ce ta 'yan aware mai suna Southern Cameroon National Council, SCNC, kuma sun yi wani taro ne a garin Buea albarkacin zagoyar ranar cika shekaru 50 da Kamaru ta samu 'yancin kai.

Kungiyar ta SCNC dai tana fafutukar ganin yankin na Kudancin Kamaru mai amfani da harshen Ingilishi, ya balle daga kasar.