Karzai zai tattauna da Pakistan

Shugaban Afghanistan, Hamid Karzai Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Afghanistan, Hamid Karzai

Shugaban kasar Afghanistan, Hamid Karzai ya shaidawa wasu shugabannin addini a Kabul cewa, hanya guda ta samun zaman lafiya a kasar ita ce ta tattaunawa da kasar Pakistan, a maimakon 'yan kungiyar Taliban.

Shugaba Karzai ya ce ba abu ne mai yiwuwa ba a gano inda majalisa ko shugaban 'yan kungiyar Taliban Mullah Omar yake.

Inda ya kara da cewa kisan tsohon shugaban kasar Burhanuddin Rabbani a farkon wannan watan da wani dan kunar bakin wake da ake zargin wakilin kungiyar Taliban ya kai, ya sa shi maida hankali wajen tattaunawa da Pakistan.

Sai dai wasu na ganin cewa wannan nauyi ba akan Pakistan kadai ya rataya ba.

Kuma an saukaka abin idan aka ce tattaunawa da Islamabad zai magance dukkanin matsalar Afghanistan da 'yan gwgwarmaya.