Sirte na bukatar kayan agaji

Wata motar sulke a garin Sirte dake Libya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wata motar sulke a garin Sirte dake Libya

Kungiyar agaji ta ICRC ta ce ana matukar bukatar kayayyakin agaji a garin Sirte dake Libya, sakamakon mummunar yanayin da ake ciki a garin da shi ne na karshe da ke hannun magoya bayan kanal Ghaddafi.

Ana dai ci gaba da tafka kazamin fada tsakanin magoya baya Gaddafi da dakarun 'yan tawayen.

Kakakin kungiyar ta ICRC Hichem Khadraoui ya ce tawagar kungiyar ta ziyarci babban asibitin dake garin a jiya asabar don kai magunguna da ledojin da ake zuba gawawwaki.

Kakakin kungiyar ya bayyana cewa ma'aikatan asibitin na Ibn Sima sun ce mutune na ci gaba da mutuwa saboda karancin iskar oxygen da kuma man fetur a injinan jenaretan asibitin.

Wasu rokokin da jiragen yakin NATO suka harba sun fada a asibitin a lokacin da tawagar kungiyar suka kai ziyarar.