An sace wata 'yar kasar Faransa a Kenya

Taswirar kasar Kenya
Image caption Taswirar kasar Kenya

Kasashen Burtaniya da Faransa sun kara fadada gargadin kan tafiye-tafiye ga 'yan kasar su zuwa yankunan arewacin Kenya bayan da aka sace wata mata wacce ke da nakasa 'yar kasar Faransa a jiya asabar.

An sace matar a wani gurin shakatawa a kusa da tsibirin Lamu kuma wadanda suka sace ta sun tafi da ita kasar Somalia.

Wannan harin dai shi ne karo na biyu da aka kai a yankin cikin makwanni uku, bayan da wasu 'yan bindiga 'yan kasar Somalia suka kashe wani dan Burtaniya tare da sace matarsa.

Harin dai ka iya haddasa koma-baya ga bangaren yawon bude ido na kasar ta Kenya.