Dubban jama'a na barin Sirte, a Libya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jerin gwanon motoci na barin birnin Sirte, Libya

Dubun dubatar 'yan Libya sun yi amfani da tsagaita bude wuta na wucin gadi, don tserewa daga birnin Sirte, daya daga cikin yankunan da magoya bayan Kanar Gaddafi suka ja daga.

Wani wakilin BBC da ke wajen birnin na Sirte, ya ce ya ga wani jerin gwanon motoci dauke da jama'a da kuma kayayyakinsu suna ficewa birnin .

Dakarun sabuwar gwamnatin Libya dai sun shafe makonni suna yi wa birnin na Sirte kawanya, a yunkurinsu na murkushe sojojin dake biyayya ga Kanar Gaddafi, amma har yanzu suna fuskantar mummunar tirjiya daga garesu.

Kungiyar agaji ta Red Cross dai ta ce mazauna birnin suna cikin wani halin kaka-na-kayi.