Najeriya za ta fara jigilar mahajjata

Tutar Najeriya
Image caption Tutar Najeriya

A Najeriya, a yau ne ake sa ran za'a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa kasar Saudi Arabia.

Kimanin maniyyata dubu casa`in da biyar daga Najeriyar ake sa ran za su tafi aikin hajjin wannan shekarar.

Sai dai a Najeriyar ba kasafai ake kammala aikin jigilar alhazan ba, ba tare da an fuskanci wasu matsaloli da suka hada da rashin isassun jirage da kuma rashin kyakkawan tanadi na jigilar maniyyatan ba.

Mahajjatan da ma sauran al'umar kasar na fatan a bana za'a samu sauyi mai kyau.