Kungiyoyin agaji sun gargadi Afghanistan

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Wasu manyan kungiyoyin agaji sun yi gargadin cewa nasarar da aka samu wajen inganta rayuwar mata a Afghanistan na fuskantar hadari.

A rahoton da kungiyar Oxfam da ta Action aid suka fitar, sunce mata da dama na cikin damuwa na cewa nasarar da aka samu a kasar za'a sadaukar da ita wajen neman cimma yarjejeniyar siyasa da kungiyar Taliban. Rahoton yace an samu nasara wajen ilimin 'ya'ya mata da harkar kiwon lafiya da ayyukanyi tun lokacin da kasashen duniya suka mamaye kasar.