Amurka na son haqqani ta tattauna da Afghanistan

Shugaban kungiyar Haqqani, Surajuddin Haqqani
Image caption Shugaban kungiyar Haqqani, Surajuddin Haqqani

Shugaban kungiyar Haqqani a Afghanistan ya ce hukumar leken asiri ta Amurka ta tuntube shi, tana so kungiyar ta tattauna da gwamnatin Afghanistan.

Suraj Haqqani ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da BBC, kodayake bai ce ga martanin da suka bayar ba.

Haka kuma ya musanta cewa kungiyar ce ke da alhakin hare-haren baya-bayan nan a Kabul.

Kuma kungiyar acewarsa ba ta karbar umarni daga hukumar leken asirin Pakistan.