Za mu sauya salon tattaunawa da Taliban

Shugaban Afghanistan Hamid Karzai, ya ce kasar sa ba za ta sake tattaunawa kai tsaye da kungiyar taliban ba domin neman zaman lafiya, sai dai nan gaba za ta rika tattaunawa ne da kasar da ke goya musu baya.

Mr Karzai ya bayyana hakan ne a wani takaitaccen jawabin da ya yi a gidan talabijin na kasar.

Wakilin BBC a yankin ya ce hakan wani hannunka mai sanda ne ga kasar Pakistan wadda Mr Karzai ke zargi da haddasa matsaloli da dama a kasarsa, ta hanyar mara wa kungiyar Taliban baya.

Shugaba Karzai ya kuma ce zai kira babban taron dattijan kasar wanda aka fi sani da Loya jigrga don tattauna makomar zaman lafiya a kasar.