Kona masallaci ya janyo tarzoma a Isra'ila

Wasu mutane sun bankawa wani masallaci wuta a wani garin Labarawa da ke arewacin Israila, inda suka haddasa barna mai muni a cikin massallacin.

Wasu Kalaman salon magana da aka rubuta a jikin masallacin da harshen Hebrew, na nuna goyan baya ga wani shirin da wasu Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi ke yi na adawa da manufar nan ta rage matsugunnan Yahudawa a yankunan Palasdinawa.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewar wadanda suka kai wannan hari sun wuce gona da iri.