An kama mutane bakwai akan harin Zamfara

'Yan sandan Najeriya
Image caption 'Yan sandan Najeriya

'Yan sanda a Najeriya sunce sun cafke mutane bakwai da ake zargi da hannu a harin da aka kai a kauyen Lingyado dake jihar Zamfara.

Kimanin mutane goma sha tara ne dai suka mutu a harin da wasu mutane kimanin dari da hamsin suka kai kauyen.

Haka kuma an jikkata wasu mutane bakwai a harin wanda aka kai a ranar Asabar din da ta gabata.

'Yan sanda dai sunce harin na daukar fansa ne.