India da Afghanistan sun kulla yarjejeniya mai dama

Shugaba Karzai da Pirayim Minista Manmohan Singh Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Karzai da Pirayim Minista Manmohan Singh

Kasashen India da AFghanistan sun kulla wata sabuwar yarjajeniya, domin fadada dangantakar da ke tsakaninsu ta fuskar tsaro da ci gaba.

An sa hannu a kan yarjajeniyar ce, a lokacin ziyarar da shugaban Afghanistan, Hamid Karzai, ya kai Indiya.

Da yake magana a Delhi Pirayim Ministan India, Manmohan Singh, ya ce yayi cikakkiyar tattaunawar gaskiya tare Shugaban na Afghansitan a kan matsalar ta'addanci a yankin.

Shugaba Hamid Karzai mai ziyara ya godewa India bisa ga kokarinta wajen kyautata zaman lafiya a yankin.

Wannan ziyara dai ta zo ne yayin da dangantaka ta tabarbare sosai tsakanin Afghanistan da Pakistan - watau dadaddiyar abokiyar gabar Indiya.